in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana kokarin samun ci gaban shawarwarin nukiliyar Iran
2015-06-29 11:01:50 cri

A yayin da ranar karshe ta kai ga cimma wata yarjejeniyar karshe kan shirin nukiliya na kasar Iran ke kusantowa, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Li Baodong ya bayyana a ranar Lahadi a birnin Vienna cewa, muna kan wasu matakai na cimma layin karshe na shawarwarin nukiliyar kasar Iran.

Tawagogin masu shawarwari na kasashe shida da suka hada da Amurka, Burtaniya, Faransa, Sin, Rasha da Jamus, da kuma kasar Iran na aiki tukuru, in ji mista Li tare da bayyana cewa, sun samu nasarori sosai, amma duk da haka, jan aiki na jiran mu, domin akwai wasu batutuwa masu sarkakiya ba tare da ba da karin haske ba kansu.

Ranar 30 ga watan Yuni na karatowa, muna fatan kai ga cimma wata yarjejeniya a lokacin, kuma muna farin ciki da ganin dukkan bangarorin da batun ya sha suna himmantuwa a cikin wadannan shawarwari, in ji mista Li Baodong bayan zuwansa a birnin Vienna.

A cewar shi, kasar Sin na kokarin ba da kwarin gwiwa ga dukkan bangarori masu ruwa da tsaki da su nuna niyyar siyasa da kuma nuna sassauci.

Wannan yarjejeniya ta karshe na da muhimmanci sosai, ga tushen muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, a yankin Gabas ta Tsakiya, har ma da duniya baki daya, a cewar mista Li.

Tawagar kasar Sin, ta zo nan da fata na gari da jajircewa. Za mu yi kokarin samun ci gaba, sannan mu cimma wata yarjejeniya ta karshe a lokacin, in ji mista Li, kafin ya kara da cewa, kasar Sin na nacewa wajen ganin an cimma wata yarjejeniyar karshe a farkon watan Yuli ba tare da wani karin jinkiri ba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China