Kasashen Iran da sauran kasashen da batun nukiliyar ya shafa suna samun ci gaba a tattaunawar wannan zagayen, in ji manyan jami'an kasashen Amurka da Iran din a ranar Laraba, kwana daya da cikar wa'adin 30 ga watan Yuni da aka diba domin cimma matsaya.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammed Javad Zarif suka bayyana hakan a birnin Vienna na kasar Austria a bayanin da suka yi wa manema labarai sun ce, akwai wassu matsaloli masu sarkakkiya, amma suna da imanin cewa, suna samun ci gaba, kuma za su ci gaba da kokari a haka.
Tun da farko ministan harkokin wajen na Iran Javad Zarif ya shaida wa manema labarai cewa, an samu ci gaba sosai, kuma za'a kara samun ci gaba, za su yi amfani da duk wata hanya da suke da ita ta ganin an samu ci gaban.
Ana sa ran ministan harkokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius da takwaransa na kasar Sin Wang Yi za su shiga cikin tattaunawar a ranar Alhamis din nan a birnin na Vienna tare da shugaban tsari na kasashen waje na kungiyar tarayyar Turai wato EU, Federica Mogherini.
Kamar yadda mataimakiyar kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Marie Harf ta sanar a ranar Talata, sabuwar tattaunawa a kan batun nukiliya tsakanin kasashen da batun ya shafa wato Britaniya, Faransa, Rasha, Sin da Jamus da ita kanta Iran din, an kara wa'adinta daga ranar 30 ga watan Yuni zuwa 7 ga watan Yuli. Kasashen dai gaba daya sun amince a kan jadawalin da aka cimma a watan Afrilu tare da kafa ranar 30 ga watan Yuni a matsayin wa'adin karshe na kammala duk wata tattaunawa bayan da aka samu tsaiko na aiwatar da taruka 2 cikin wa'adin watan Yuni da na Nuwambar bara. (Fatimah)