Shugaba Hassan Rouhani na kasar Iran ya ce, Iran din za ta warware sauran batutuwa masu sarkakiya da suka rage game da batun nukiliyar kasar yayin wani shawarwari da hukumar kula da harkokin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA) a wani lokaci da sassan biyu suka tsayar.
Shugaba Rouhani wanda ya bayyana hakan yayin ganawarsa da shugaban hukumar ta IAEA Yukiya Amano da ke ziyara a kasar, ya kuma bayyana cewa, kasarsa a shirya take ta warware muhimman batutuwan da suka rage kamar yadda ke kunshe cikin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukuliya (NPT).
Shugaba Rouhani ya ce, kamata ya yi hukumar IAEA ta taka rawar da ta dace kan batun nukuliyar kasar da manyan kasashen duniya da batun ya shafa ba tare da nuna wani son kai ba.
A jawabinsa, shugaban hukumar IAEA Yukiya Amano ya ja kunno Iran da kada ta kera makaman nukiliya. Ya kuma yi imanin cewa, za a warware ragowar matsalolin ta hanyar yin shawarwari.(Ibrahim)