Rahotanni daga Nigeriya sun tabbatar da cewa, a kalla mutane 30 ne suka hallaka sakamakon wani hari da 'yan bindiga wadanda suka farma wani kauye a jihar Benue suka kai.
Yan bindigan sun afka wa kauyen Iorza ne da sanyin safiyar Lahadi, suka rika harbi kan mai uwa da wabi, in ji Austin Ezeani, kakakin 'yan sandan jihar, a bayanin da ya yi wa manema labarai, sai dai ya ce, ya zuwa wancan lokacin dai gawawwaki 4 aka gani.
Daya daga cikin mazauna kauyen John Kaaba wanda ya shaida hakan ya tabbatar wa Xinhua da an hallaka mutane 30 lokacin da maharan suka afka wa kauyen, galibinsu mata da yara kanana da kuma tsofaffi.
Ya ce, mutane da dama sun ji rauni sosai kafin jami'an tsaro su kawo dauki komai ya lafa. Yanzu wadanda suka ji raunin suna asibiti a kusa da Makurdi, babban birnin jihar.
Sai dai ba'a tabbatar da ko mayakan Boko Haram ne suka kai harin ba, wassu kuma suna ganin makiyaya ne ke tada rikici a kauyen. (Fatimah)