in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karancin abinci na tsananta a kasashen Afirka da na Gabas ta Tsakiya, in ji FAO
2014-12-12 10:56:16 cri

Wani sabon rahoto da hukumar samar da abinci da ayyukan gona ta majalisar dinkin duniya FAO ta fitar, ya nuna cewa, kasashen dake nahiyar Afirka, da na Gabas ta Tsakiya ne suka fi fuskantar barazanar karancin abinci. Lamarin da rahoton ya alakanta da matsalolin tsaro, da sauyin yanayi da kuma bullar cutar Ebola.

Rahoton wanda FAO ta fitar a jiya Alhamis ya kuma yi kashedin cewa, rashin kyawun yanayi a wasu yankunan Sahel zai iya haifar da raguwar albarkatun gona, inda hasashe ke nuna a kasar Senegal, mai yiwuwa a samu raguwar da ta kai kaso kusan 38 bisa dari.

Game da matsalar tsaro kuwa, FAO ta ce, tashe-tashen hankula musamman a kasar Syria, na dada gurgunta harkokin noma a yanzu haka, matakin da ya sanya kusan mutane miliyan 6.8 fadawa cikin matsalar karancin abinci.

Baya ga Syria ita ma kasar Iraq na fuskantar makamanciyar wannan matsala, inda ya zuwa shekarar da ta gabata, yawan 'yan gudun hijirar kasar ya ninka kusan sau 3.

Wannan rahoto na FAO ya kuma ayyana kasashen janhuriyar Afirka ta Tsakiya, da yankin Dafur na kasar Sudan, da Sudan ta Kudu, da Somaliya a matsayin kasashen da su ma ke fuskantar tarin matsalolin abinci a nahiyar Afirka. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China