Kamfanin sadarwar zamani wato ICT, Huawei na kasar Sin dake da reshe a kasar Ghana ya yi cinikin kusan dalar Amurka 305, in ji wani jami'in ofishin, wanda ya ce wannan ya samar da ayyukan yi fiye da 4,000 a wannan fanni.
Archur Zhou, darektan bangaren kasuwanci na Huawei a Ghana ya bayyana hakan ne game da shirin kaddamar da baje kolin wayoyi da harkokin sadarwa na zamani a Ghana karo na farko da za'a yi a wata gobe.
A cewar shi, kamfaninsa na sadarwar zamanin a Ghana yanzu haka yana da ma'aikata 700, kuma kashi 75% mazauna wajen ne, kuma tun daga shekara ta 2005 zuwa yanzu, sun samu ci gaba sosai a kasar ta Ghana, abin da ya sa a cikin shekarun da suka gabata, sun kaddamar da ayyuka da dama tare da gwamnatin kasar ta Ghana.
Ya ce, kamfanin ya yi aiki da wassu manyan kamfanonin sadarwa na kasar kan bullo da tsarin fasahohin ci gaba a wannan bangaren.
A cewar darekta Zhou, kamfanin Huawei ba kawai kasuwanci yake yi ba, har ma daga cikin shirin sa shi ne kyautata rayuwan al'ummar ta hanyar sadarwar zamani, kuma hakan a bayyane yake a harkokin cinikinsa da sauke nauyin da ya rataya a wuyansa. (Fatimah)