Kamfanin sarrafa karafa na Sentuo dake kasar Ghana, ya sha alwashin fadada kasuwarsa zuwa sassa daban daban na yammacin Afirka, bayan shafe shekaru 4 yana cinikayya a kasar ta Ghana.
A cewar manajan daraktan kamfanin Xu Ningquan, ci gaban da kamfanin ya samu a baya bayan nan, ya biyo bayan sayen kamfanin Wahome da suka yi, kamfanin da ke iya sarrafa karfe har sama da tan 300,000.
Mr. Xu ya ce, Sentuo ya shigar da jari har dalar Amurka miliyan 48, tare da daukar ma'aikata 600 a wani mataki na fadada ayyukansa.
Bugu da kari bisa burin fadada kasuwar kamfanin, Mr. Xu ya ce, yanzu haka sun kammala sashe na biyu na masana'antar, sashen da zai fara aiki nan da dan lokaci. Ya ce, kamfanin tare da sauran masu zuba jari ne suka sanya makudan kudade domin gina sashen na biyu, wanda zai kasance irin sa na farko a dukkanin fadin nahiyar yammacin Afirka. (Saminu)