in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana jiran sabuwar gwamnatin Burkina Faso nan da sa'o'i 72
2014-11-21 10:48:17 cri

Laftanal kanal Isaac Yacouba Zida da shugaba Michel Kafando ya nada a matsayin sabon faraministan wucin gadi a ranar Laraba, ya bayyana a daren wannan rana cewa, gwamnatinsa za ta bayyana nan da sa'o'i 72 masu zuwa.

Za'a gabatar da sabuwar gwamnatin wucin gadi nan da sa'o'i 72 masu zuwa, in ji mista Zida a gaban manema labarai. Laftanal kanal Zida ya karbi iko a karshen watan Oktoba bayan faduwar Blaise Compaore sakamakon bore na al'ummar kasar.

Wannan zabi ya bayyana yardar da aka nuna wa jami'an tsaron kasar baki daya, a wannan muhimmin lokaci na tarihin kasarmu. Ina la'akari da babban nauyin da aka ba ni na jagorantar gwamnati, wadda makasudinta na farko shi ne, na shirya zabubuka cikin adalci, bisa tushen gaskiya da 'yanci, har ma da kawo wasu muhimman sauye-sauye domin makomar kasarmu, in ji mista Zida, wanda a Talata aka ba shi lambar yabo mafi daraja ta kasar daga hannun babban alkalin kasar Burkina Faso. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China