in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An amince da ci gaba da tattaunawa game da rikicin siyasar Libiya cikin kasar
2015-01-30 09:39:25 cri

Wakilai mahalarta taron warware rikicin siyasar kasar Libiya, sun amince da gudanar da taronsu na gaba a cikin kasar, bayan kammala zagaye na biyu na tattaunawarsu a ofishin MDD dake birnin Geneva.

Mahalarta taron sun hada da wakilan gundumomi, da na kananan hukumomin kasar ta Libiya, da kuma wakilin musamman na babban magatakardar MDD a kasar Bernardino Leon.

Cikin jawabin da ya gabatar yayin zaman, Mr. Leon ya yi wa wakilan majalissun al'ummar kasar karin haske, game da tsarin wanzar da sulhu da ake da muradin aiwatarwa.

A wani ci gaban kuma, wata sanarwa da ofishin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD a Libiya UNSMIL ta fitar, ta tabbatar da amincewar da aka yi na a ci gaba da tattaunawa cikin kasar ta Libiya, muddin dai akwai kyakkyawan yanayin tsaro.

Sanarwar ta kuma bayyana bukatar da UNSMIL ta gabatar ga daukacin masu ruwa da tsaki game da rikicin siyasar Libiyan, da su hada kai da juna domin tabbatar da nasarar da aka sanya gaba.

A daya bangaren kuma, mahalarta taron da ya gabata sun yi Allah wadai da harin baya bayan nan da aka kaddamar a birnin Tripolin kasar ta Libiya, suna masu cewa, duk da yanayin da ake ciki, bai kamata a yi watsi da damar da ake akwai, ta kokarin warware matsalar kasar cikin lumana ba. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China