in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Musulmi a kasar Sin) Kamfanonin samar da kayayyakin halittu na halal dake kan hanyar siliki
2015-07-15 13:16:43 cri

A shekarar 2014, yawan kayayyakin da masana'antar kamfanin Amin dake unguwar Honggu ta birnin Lanzhou ta kera ya kai kudin Sin RMB Yuan miliyan 250. Babbar nasarar da kamfanin Amin ya samu ta ba da kwarin gwiwa sosai ga jami'an yankin kayayyakin halittu na halal na unguwar Honggu, wadanda sun yi imani sosai kan kyakkyawar makomar sana'ar kera kayayyakin halittu na halal. Mataimakin shugaban unguwar Honggu mai kula da tattalin arziki Wang Zhengxiang ya bayyana a yayin da yake ganawa da manema labaru cewa, "shirin ziri daya da hanya daya" zai kawo sabon zarafi ga bunkasuwar kamfanonin yankin, za a kyautata tsarin kamfanonin yankin kayayyakin halittu na halal a nan gaba. A game da haka, ya ce,"Ana kokarin raya yankin kayayyakin halittu na halal zuwa yanki iri na zamanance dake da jerin kamfanonin da za su iya kawo moriyar juna, haka kuma, wannan ra'ayi ya dace da 'shirin ziri daya da hanya daya'. A nan gaba, za a kara jawo karin kamfanoni da su zuba jari a yanki, ciki har da kamfanonin kiwon dabbobi da samar da kayayyakin nama da kera kayayyakin abinci da maguguna da kuma kayayyakin kiwon lafiya, domin raya jerin kamfanonin kayayyakin halal a yankin."

Bugu da kari, Wang Zhengxiang ya ce, yankin kera kayayyakin halittu na unguwar Honggu zai yi amfani da kwarewarsa wajen kyautata zirga-zirga da sufuri da sauran manyan ayyukan yau da kullum bisa tsarin da aka tsara a sassa daban daban na yankin. Kana za a yi amfani da manufofi masu gatanci da gwamnatin Sin ta gabatar wa yankunan cinikayya dake wuraren da ba su dab da teku, domin habaka kasuwanni ga kamfanonin dake kan hanyar siliki.(Lami)


1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China