(Musulmi a kasar Sin) Kamfanonin samar da kayayyakin halittu na halal dake kan hanyar siliki

Yankin kamfanonin samar da kayayyakin halittu na halal na unguwar Honggu dake birnin Lanzhou yana kasancewa a yankin kogi dake arewa maso gabashin tudun Qinghai-Tibet. Inda ya taba zama wata muhimmiyar tashar dake kan kudancin hanyar siliki a cikin tarihi, kuma har illa yau, ya ci gaba da zama muhimmin wurin da hanyoyin mota da na jiragen kasa suka ratsa zuwa tudun Qinghai-Tibet. Duk da cewar tsayinsa ya kai fiye mita da dubu 2, kuma yankinsa na fama da mummunan yanayi, amma hakan ba su hana bunkasuwar jerin sabbin kamfanonin samar da kayayyakin halal a wannan wurin ba.
"An kafa wannan kamfani cikin dan kankanan lokaci, cikin kwanaki 475 kawai aka kammala sa, saurin kafuwarsa ta fi ta sauran kamfanonin kasar Sin. An cimma babbar nasarar gwajin aiki da kuma bude kamfanin."
1 2 3 4