in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Musulmi a kasar Sin) Kamfanonin samar da kayayyakin halittu na halal dake kan hanyar siliki
2015-07-15 13:16:43 cri

Zhang Haining mai shekaru fiye da 40 da haihuwa shi ne shugaban masana'antar samar da kayayyakin halal ta Amin dake unguwar Honggu, wanda yake gudanar da wannan aiki har fiye da kusan shekaru 20. Ya na alfari sosai a yayin da yake magana kan ayyukan da ya yi wajen kafa wannan masana'anta. Ya ce, a lokacin da, mun sarrafa kayayyakin da hannayenmu, amma a halin yanzu, muna amfani da na'urori wajen samar da wadannan kayayyaki. Ba ma kawai yanayin aikinmu ya samu kyautatuwa ba, hatta ma ya taimaka wajen kawar da mummunan tasirin da yanayin tudu ya kawo mana.

Masana'antar da na ambata a farko ita ce reshen kamfanin Amin wanda hedkwatarsa take a birnin Shanghai, an zuba jarin da yawansa ya kai kudin Sin RMB Yuan miliyan 200 domin kafa wannan masana'anta a unguwar Honggu ta birnin Lanzhou. Kamfanin Amin shi ne wani kamfanin samar da kayayyakin halal mafi girma anan kasar Sin, shugaban kamfanin Su Han ya bayyana cewa,"Mun bambanta sosai da sauran kamfannoni, muna sarrafa kayayyakin halal kawai, muna fidda abubuwan da muke bukata daga saniya da tumaki, wannan shi ne babban aikin da muke gudana a kowace rana."

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China