in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Musulmi a kasar Sin) Kamfanonin samar da kayayyakin halittu na halal dake kan hanyar siliki
2015-07-15 13:16:43 cri

Dole ne mu samar da kayayyakin halal bisa ka'idar musulunci, musulmai biliyan 1.5 daga kasashe mambobi fiye da 50 da yankunan kungiyar kasashe musulumi suna bukatar kayayyakin halal masu dimbin yawa. Amma a halin yanzu, galibin wadannan kasashe ba su da fasahohin samar da kayayyakin da suke bukata.

Su Han ya nuna cewa, yankin samar da kayayyakin halal na unguwar Honggu yana arewa maso gabashin tudun Qinghai-Tibet, wanda yana da tsayi sosai, shi ya sa, ana da isashen hasken rana, kuma iska ba ta da raba sosai, hakan ya aza harsashi ga aikin cire robar halittu daga kashin saniya. Ban da haka kuma, kamfanin Amin wani kamfani ne da ya samu tasiri sosai daga "shirin ziri daya da hanya daya", abubuwan da ya kawo da kuma kayayyakin da yake fitar sun dogara ne kan kasuwannin hanyar siliki. Mr. Su ya kara da cewa,"Mun kafa kamfaninmu a shekarar 2010 tare nufin fitar da kayayyakinmu zuwa kasashen dake kan hanyar siliki. Yanzu haka, mun samu kwarin gwiwa sosai bayan da gwamnatin kasar Sin ta gabatar da 'shirin ziri daya da hanya daya'. Wadannan kasashe da kasar Sin suna taimakawa juna, alal misali, mun fitar da kayayyakin halittu na halal da suke bukata, kuma mun shigo da kashin saniya da sauran abubuwan da muke bukata domin kera kayayyaki."

An ba da labari cewa, kayayyakin halittu na halal da kamfanin Amin ya kera sun samu karbuwa sosai daga musulman kudu maso gabashin Asiya da yankin gabas ta tsakiya. Alal misali, an fitar da furoti da sauran kayayyakin halal zuwa kasashen Malaysia da Masar da Iran da kuma Turkiyya da dai sauransu. An kirkiro sabbin kayayyaki da kuma gudanar da manyan ayyukan kamfanin Amin a hedkwatarsa dake birnin Shanghai, daga bisani, masana'antar kamfanin dake unguwar Honggu ta birnin Lanzhou ya dukufa kan shigo da kashin saniya daga tudun Qinghai-Tibet da kuma kasashen Bangladesh da Australia, ban da haka kuma, kamfanin ya kafa cibiyar sayar da kayayyakinsa a kasar Malaysia da kuma wani kamfanin wakilkcinsa a kasar Indonesia domin sayar da kayayyakin halal nasa a kasashen musulumi.

1 2 3 4
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China