in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
INEC a Togo ta karbi sunayen 'yan takarar shugabancin kasa 5
2015-03-04 09:45:58 cri

Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta ta kasar Togo INEC, ta ce, ta karbi sunayen masu sha'awar tsayawa takarar shugabancin kasar, yayin babban zaben kasar da ke tafe cikin watan Afirilu mai zuwa.

Wata sanarwa da hukumar ta INEC ta fitar, ta ce, 'yan takarar 5 su ne Jean-Pierre Fabre na jam'iyyar CAP 2015, da Faure Gnassingbe Essozimna na UNITE party, da Gogue Tchaboure na jam'iyyar ADDI. Sauran su ne Taama Komandega na NET, da kuma Traore Tchassona Mouhamed na jam'yyar MCD.

Sanarwar ta kuma ce, bisa dokar zabe, hukumar za ta tantance takardun bukatar da 'yan takarar suka gabatar, kafin daga bisani kotun tsarin mulkin kasar ta zayyana wadanda suka cancanci shiga takarar cikin kwanaki 25 masu zuwa. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China