in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi maraba da matakan da Cote d'Ivoire ta dauka na kawo karshen lalata da yara
2015-06-26 09:52:00 cri

Wakiliyar musamman ta babban sakataren MDD mai kula da laifukan yin lalata da yara a lokacin yaki, Zainab Hawa Bangura ta yi maraba da sabbin matakan da kasar Cote d'Ivoire ta dauka na kawo karshen yadda ake lalata da yara a lokutan yaki.

Ta ce, matakin da kwamandojin dakarun kasar (FRCI) 47 suka dauka zai taimaka wajen kawo karshen wannan ta'asa tare da tabbatar da kare dokokin jin kai da na 'yancin dan-Adam na kasa da kasa.

Madam Zainab Hawa Bangura ta kara da cewa, wannan wani kwakkwaran mataki ne da kasar ta dauka na dorawa kan irin nasarorin da aka cimma a baya, a kokarin da ake na kawo karshen tashin hankali, sannan wajibi ne dakarun su kawo karshen yadda sojoji ke amfani da kakinsu wajen cin zarafin yara a lokutan yaki ko tashin hankali.

A watan Afrilun shekarar 2004 ne kwamitin sulhun MDD ya kafa rundunar wanzar da zaman lafiya a kasar ta Cote d'Ivoire UNOCI wadda aka dora mata alhakin ganin an aiwatar da yarjejeniyar da bangarorin siyasar kasar suka rattabawa hannu a watan Janairun shekarar 2003.

Sannan bayan tashin hankalin siyasar da ya biyo bayan zaben shugaban kasar na shekarar 2010, an dora wa rundunar  UNOCI alhakin kare rayukan fararen hula, samar da kyawawan ofisoshi, taimakawa gwamnati kwance damarar makamai, wargaza kungiyoyin dakaru masu dauke da makamai, da yiwa bangaren tsaron kasar gyaran fuska, da kuma sa-ido kan yadda ake kare hakkin dan Adam a kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China