in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara bincike game da zargin da aka yiwa rundunar sojin Najeriya
2015-06-25 10:32:26 cri

Mahukuntan Najeriya sun ce, an fara gudanar da bincike game da zargin da kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta yi wa rundunar sojin kasar, na keta hakkokin dan Adam yayin da take yaki da kungiyar Boko Haram.

Wata sanarwa da aka fitar a jiya Laraba, ta rawaito babban sakatare a ma'aikatar harkokin wajen kasar Bulus Lolo, na cewa zarge-zargen na Amnesty International na da girman gaske. Don haka ya zama wajibi a yi buda na tsanaki a kan su

Mr. Lolo ya ce, bisa dokokin da suka shafi ayyukan soji, kwarewa da sanin makamar aiki na kan gama, wanda hakan ya sanya rundunar fara gudanar da bincike kan wadancan zarge-zarge, da nufin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Sai dai a daya hannun Lolo ya ce, sojojin na da wani iko, na gudanar da wasu nau'o'in ayyuka a jihohin da aka kafa wa dokar ta baci, ciki hadda damar gudanar da tambayoyi, da tsare duk wani farar hula da ake zargi da hannu cikin ayyukan ta'addanci. Sai dai a cewarsa, duk da irin wannan dama da sojin ke da ita, gwamnati za ta tabbatar da an hukunta wadanda suka wuce gona da iri wajen gudanar da ayyukansu, domin tabbatar da kare hakkokin al'ummar kasar yadda ya kamata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China