Babban bankin Najeriya (CBN) ya fitar a ranar Laraba da wata sabuwar takardar kudi 'yar Naira 100 domin tunawa bikin da cikon shekaru 100 da hadewar tsarin mulkin arewa da kudancin kasar mafi yawan jama'a a nahiyar Afrika da shugabannin mulkin mallaka suka yi a shekarar 1914.
An gabatar da sabuwar takardar kudin a yayin zaman taron kwamitin zartaswa na tarayya (FEC) da shugaba Goodluck Jonathan ya jagoranta a fadar shugaban kasa dake Abuja, babban birnin wannan kasa dake yammacin Afrika. Sabuwar takardar kudin za ta maye gurbin ta yanzu 'yar Naira 100. A yayin bikin gabatar da sabuwar 'yar Naira darin, gwamnan bankin CBN, mista Godwin Emefiele, ya bayyana cewa, sabuwar Naira dari na da kariyar hana satar fasaha. (Maman Ada)