Kamfanin gine gine na kasar Sin, China Harbor Engineering Company (CHEC) ya lashe wata kwangilar gina wata sabuwar tashar ruwa a birnin Atuabo, mai tazarar kilomita 326 daga yammacin Accra, hedkwatar kasar. Tashar ruwan dai za ta kunshi wani mashigin ruwa mai zurfin mita 18,5, da wasu wuraren fakin jiragen ruwa guda uku masu zurfin mita 16,5, mita 12 da mita 9, har ma da wasu yankunan gudanar da ayyukan da suka shafi jigilar kayayyakin kan teku, gyare gyaren jiragen ruwa, wani bangaren kimiyya da fasaha, da wasu sauran gine ginen ba da tallafi ga ayyukan wannan tashar ruwan. (Maman Ada)