Kamfanin kasar Sin Hanergy Group zai saka kudi har dalar Amurka biliyan 1 wajen gina tashar samar da wutar lantarki ta hasken rana mai karfin megawatts 400 ga kasar Ghana.
Kamar yadda Zhou Youbin, wani babban jami'i a ofishin jakadancin kasar Sin dake Ghana ya tabbatar lokacin wani taron yini daya a kan albarkatun kasa, ya ce, kasar Sin a matsayinta na kawar Ghana bisa ga zumuncin gargajiya da kuma muhimmiyar kawa a al'amurran ci gaba ba za ta yi kasa a gwiwwa ba wajen taimaka wa duk wani aikin ci gaba da kuma gina kasar.
A wajen wannan taron karkashin taken albarkatun kasa, mulki da tafiyar da shi don ci gaba da kuma gina Ghana, Mr Zhou ya lissafta ayyuka da dama da gwamnatin kasar Sin ta aiwatar a kasar da suka hada da cibiyar iskar gas ta Western Corridor, gina madatsar ruwa Bui mai samar da lantarki har megawatts 400, da kuma fadada tashar ruwan Kpong.
Ya jaddada cewar, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da gine a kan bukatun mazauna dake wuraren albarkatun kasa.
A don haka ya ce, kwararru 'yan Afrika 300,000 suna samun horo a karkashin shirin masana a bangarori da dama. (Fatimah)