Kungiyar kwallon kafa ta Nigeriya "Super Eagles" za ta tashi a ranar Lahadin nan zuwa kasar Ingila don buga kwallon kawance tsakanin ta da Scotland.
Kakakin hukumar kwallon kafa ta kasar NFA Ademola Olajire ya ce, manyan 'yan wasa biyar daga kasar da tawagar masu horar da su za su tafi Craven Cottage, a birnin London domin wasan.
A cewar Ademola Olajire, 'yan wasan Nigeriya dake bugawa a kasashen waje za su hadu da wadannan 'yan wasa na gida a London, ya yi bayanin cewa, kungiyar 'yan wasan har ila yau za ta kara da kasar Girka a birnin Philadephia na Amurka a ranar 3 ga watan gobe na Juni, sannan za su kara da Amurkan a Jacksonville na kasar a ranar 7 ga wata, kafin su dunguma zuwa Sao Paulo na kasar Brazil a ranar 10 ga wata. (Fatimah)