Hukumar tarayyar Turai (EU) ta kara samar da Euro miliyan 21 don taimakawa al'ummomin da ke Najeriya da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita da hare-haren mayakan Boko Haram suka shafa.
Wata sanarwa da sashen agazawa kasashen ketare na hukumar ya fitar, ta bayyana cewa, sabon tallafin gaggawan ya kunshi samar da ruwan sha mai tsafta, abinci, matsuguni, kiwon lafiya da samar da kariya ga mutanen da suka rasa gidajensu.
Kwamishinan hukumar EU mai kula da harkokin jin kai da daidaita bala'u Christos Stylianides ne ya bayyana hakan lokacin da ya ziyarci Najeriya don kimanta yanayin jin kan da jama'ar ke ciki.
Jami'in na EU ya ce, sama da mutane miliyan 1.7 ne mayakan na Boko Haram suka raba da gidajensu.
Kimanin Euro miliyan 12.5 ne hukumar ta EU za ta kashe a harkokin da suka shafi jin kai a Najeriya kadai, baya ga Euro miliyan 8.5 da hukumar za ta kashe wajen tallafawa 'yan gudun hijirar da ke tsugune a kasashen Nijar, Kamaru da kuma Chadi.(Ibrahim)