Shugaban majalisar dokokin kasar Cote d'Ivoire Guillaume Soro ya yi kira a ranar Litinin a birnin Porto-Novo, hedkwatar siyasar kasar Benin, ga shugabannin siyasar Afrika da su mai da martani mai karfi na hadin gwiwa domin yaki da kungiyar Boko Haram ta Najeriya.
Wannan martanin hadin gwiwa da ya kamata mu shirya, zan kira shi "garkuwar tsaro," in ji mista Soro a yayin bikin rantsar da sabon shugaban majalisar dokokin kasar Benin, Andrien Houngbedji.
Mista Soro ya bayyana cewa, nauyi ya rataya ga dukkan wakilan jama'a da su fadakar da al'ummoninsu ta hanyar wani sakon ba ja da baya domin janyo hankalin mutanen da ake saurin juya tunaninsu kan dabarar farfagandar masu kaifin kishin islama.
Nauyin mu, shi ne mu ba da shawarar cewa, kada mutane su yi tunanin cewa, akwai kasashe da suka tsira. Annobar Boko Haram na yaduwa a ko'ina, har ma zuwa kasashen da tun fil azal ake yaba zaman lafiyarsu, in ji Guillaume Soro.
A nasa bangare, sabon shugaban majalisar dokokin kasar Benin, Andrien Houngbedji, ya nuna cewa, wannan matsala ta karuwar masu kaifin kishin islama, na jan hankalin shugabannin siyasar Afrika, har ma da mambobin kungiyoyin fararen hula na Afrika. (Maman Ada)