Shugaban tarayyar Najeriya Dr. Goodluck Jonathan, ya yi Allah wadai da hare-haren ta'addanci dake aukuwa a arewacin Najeriya.
Shugaban wanda ya bayyana takaicin asarar rayukan da wadannan hare-hare suka haddasa cikin wata sanarwa da fadarsa ta fitar, ya ce, mayakan Boko Haram na kaddamar da hare-hare ne tsakanin fararen hula, sakamakon yadda ake samun nasarar fatattakar su daga sansanoninsu.
A ranar Litinin da Talata ne dai wasu 'yan kunar bakin wake suka tashi wasu bama-bamai a birnin Potiskum, fadar mulkin jihar Yobe, lamarin da ya haddasa kisan mutane da dama. Kana a ranar Talata wasu 'yan kunar bakin waken suka hallaka kan su da wasu mutane da dama, sakamakon bam din da suka tayar a wata tashar mota dake jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa, adadin wadanda hare-haren na baya bayan nan suka hallaka sun kai mutane 50, baya ga wasu da dama da suka jikkata. (Saminu)