Jami'an tsaron kasar Somaliya a ranar Talatan nan suka kaddamar da wani samame a Mogadishu, babban birnin kasar, da zummar kakkabe mayakan Al-Shabaab wadanda ake zargin suna boye a wassu gidajen dake cikin birnin, kamar yadda rundunar 'yan sanda suka tabbatar.
Samamen na hadin gwiwwa tsakanin jami'an tsaron Somaliya da na kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU wato AMISOM, an fara shi ne da safiyar wannan rana, kuma an yi nasarar damke wassu 'yan kungiyar da dama da 'yan sandan bisa bayanin da suka samu na sirri ke nuna cewa, suna shirin kai hari a cikin birnin.
Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Mohammed Yusuf ya ce, bayanin sirri ya tabbatar da cewar, wassu 'yan kungiyar ta Al-Shabaab sun shigo birnin a asirce, kuma suna zaune a wassu rukunin gidaje, inda suke shirin kaddamar da hare-hare.
Mohammed Yusuf ya kara da cewa, hukumomin tsaro za su ci gaba da ayyukansu ba da gazawa ba domin tabbatar da birnin ya samu kariya, yana mai gode wa al'umma mazauna bisa ga hadin kan da suke ba su da kuma samar da bayanai. (Fatimah)