in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin yaki da cin zarafin jama'a na MDD ya kammala nazarin da ya ke kan Amurka
2014-11-14 10:12:16 cri

A jiya ne kwamitin nan da ke yaki da gallazawa jama'a na MDD ya kammala nazarin da yake game da yadda Amurka ta aiwatar da matakan gallazawa mutanen da ake tsare da su.

Yayin zaman kwamitin na yini biyu, tawagar Amurka ta amince cewa, tana cin zarafin mutanen da ake tsare da su ta hanyoyi daban-daban, kuma ba ta sake nazartar wadannan matakai ba tun shekarar 2006. Tana mai jaddada cewa, Amurka ta dauki matakan da suka dace wajen tabbatar da bin dokokinta na shari'a.

Mai rikon mukamin mai baiwa shugaba Obama shawara kan harkokin shari'a ta ma'aikatar harkokin wajen Amurka, kana wakiliya a tawagar ta Amurka a ganawar Mary McLeod, ta bayyana yayin zaman cewa, Amurka ta bullo da wadannan matakai ne bayan harin 11 ga watan Satumba da aka kaiwa Amurka da nufin kare muradunta.

Abubuwan da kwamitin ya fi mayar da hankali a kai sun hada da fursunonin da ake tsare da su a Guantanamo ba tare da an yanke musu hukunci ba, wuraren da hukumar CIA ke tsare da mutane a asirce, dokokin da suka shafi bakin haure, yadda 'yan sanda ke cin zarafin mutane da sauran nau'o'in cin zarafin mutane. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China