Kungiyar Boko Haram da ke kai hare hare a yankunan arewa maso gabashin Najeriya ta zama babbar barazanar dake ci gaba da kawo illa ga zaman lafiya da tsaron Najeriya, har ma da shiyyar yammacin Afirka baki daya, tare kuma ga kasashen Kamaru, Chadi da Nijar, in ji kungiyar tarayyar Turai (EU).
A cikin wata sanarwa da aka fitar bayan taron ministocin kungiyar a birnin Bruxelles, shugabannin diplomasiyar kasashe 28 sun jaddada muhimmancin daukar matakan gaggawa, domin hana Boko Haram ci gaba da aikata harkokin ta'addanci da munanan laifuffuka.
Shugabannin EU sun yi allawadai da hare hare da tashe tashen hankali da kungiyar Boko Haram kan fararen hula, da yawancinsu mata ne da kananan yara. Ministocin harkokin wajen tarayyar Turai sun yi kira ga kasashen dake fama da matsalar Boko Haram da su kara karfafa dangantakarsu da daidaita ayyukansu. Haka kuma shugabannin sun yi maraba da taimakon rundunar sojojin kasar Chadi da na Kamaru da tuni suke yaki da Boko Haram. Tare da bayyana goyon bayansu ga matakin kasashen shiyyar, tare da hadin gwiwa tarayyar Afrika (AU) na tura wata rundunar kasa da kasa.
Kwamitin harkokin wajen tarayyar Turai ya dauki niyyar tallafawa shiyyar da kayayyakinsa, musammun ma wajen taimakawa kasashen da matsalar ta shafa karfafa karfinsu domin fuskantar kalubalolin ta'addanci da tashe tashen hankali, ta hanyar ba da goyon baya wajen karfafa dangantakar tsakanin wadannan kasashe. (Maman Ada)