Musulmai a kasar Chadi sun fara azumi na wata mai tsarki, amma kuma ba za su sanya nikab ko burka da rawani, da wasu alamomi da za su rufe fuska baki daya, kamar yadda karin matakan tsaron suka tanada da gwamnatin kasar ta dauka bayan wasu jerin hare haren kunar bakin wake biyu da aka kai a N'Djamena, babban birnin kasar a ranar Litinin.
Sanya nikab ko burka, ko ma rawani da wasu alamomin da ke rufe fuska baki daya, ana iya daukar sa a wani matsayin shiddabaru ne na kai hari, don haka an hana, in ji faraministan kasar Chadi, Kazeube Payimi Deubet, a yayin wani zaman taro tare da shugabannin addinai daban daban.
Dole a daina sanya burka nan take tun daga wannan rana, a cikin wuraren jama'a, makarantu, har ma a dukkan fadin kasar, in ji Payimi Deubet, kafin ya bukaci shugabannin da su isar da wannan sako a cikin wuraren ibada da masallatai.
Duk wadanda suka bijirewa wannan doka suka sanya burka ko rawani, to za'a cafke su, a yi musu shari'a, sannan a yanke musu hukunci, in ji mista Payimi Deubet cikin wani kashedi, tare da bayyana cewa, an baiwa jami'an tsaro umurnin shiga cikin kasuwanni su karbe dukkan nikab ko rawani da ake sayarwa domin a kona su. (Maman Ada)