in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sanar da fara azumin Ramadan a Nigeriya
2015-06-18 13:58:17 cri

Majalissar koli ta harkokin addinin musulunci a Nigeriya ta umurci daukacin musulman kasar da daukan azumi a yau Alhamis din sakamakon ganin watan Ramadan da ya yi.

Hakan ya biyo bayan sanarwar da sarkin musulmin kuma shugaban majalissar kolin harkokin addinin musuluncin kasar Sultan Sa'ad Abubakar III wanda hakan ya zama azumi na shekarar 1436 bayan hijira.

Sultan Sa'adu Abubakar ya sanar da ganin sabon watan a wurare da dama da sarakunan garuruwan suka tabbatar, sannan ya ba da umurnin daukan azumin a jawabin da ya yi kai tsaye ga al'ummar musulmin kasar ta kafofin watsa labarai.

A cikin jawabin nashi, ya bukaci mabiya addinin musulunci da su kara mai da hankalinsu wajen ibada da yin addu'o'i ga sabuwar gwamnatin kasar wajen samun nasarar tafiyar da ragamar shugabancin al'umma.

Sarkin musulmi Abubakar ya kuma yi kira ga musulmai da su yi amfani da wannan wata mai albarka wajen kara bin koyarwar addinin na zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da kowa ba tare da la'akari da addini ko kabilarsa ba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China