in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shekara-shekara na kungiyar AU
2015-06-08 10:08:51 cri

An bude taron shekara-shekara na kungiyar hadin kan Afirka ta AU karo na 25 a birnin Adis Ababan kasar Habasha. Ana kuma sa ran taron na bana zai mai da hankali ga batutuwan da suka jibanci bunkasa rayuwar mata, da kuma ci gaban nahiyar.

A bana an sanyawa taron na AU taken "shekarar habaka rayuwar mata, da cimma kudurorin bunkasar Afirka nan da shekarar 2063".

Da yake jawabi gaban mahalarta taron, mamban a kwamitin wakilan din din din na kungiyar, kuma jakadan kasar Zimbabwe Albert Ranganai Chimbindi, bayyana dacewar taken taron ya yi, yana mai cewa, adadin yawan matan Afirka ya dara rabin jimillar al'ummar nahiyar, kuma su ne ke samar da kaso 75 bisa dari na kwadago da ake bukata a fannin noma a nahiyar, don haka ya zama wajibi a baiwa ci gaban rayuwar su kulawar da ta dace.

Ya ce, lokaci ya yi da Afirka za ta zage damtse wajen samar da daidaito tsakanin jinsin zama da mata, matakin da a cewarsa zai haifar da gagarumin ci gaba ga nahiyar a fannoni da dama, ciki hadda fannin tattalin arziki.

A nasa jawabi, mataimakin shugaban kwamitin wakilan din din din na kungiyar ta AU Erastus Mwencha, cewa ya yi, a wannan karo ajandar taron ta kunshi batun bunkasa tattalin arzikin Afirka, da inganta samar da ababen more rayuwa, da yaki da talauci, tare da daukar karin matakan tabbatar da tsaro, da wanzar da zaman lafiya. Ya ce, za kuma a mai da hankali kan batun yaduwar ayyukan ta'addanci a nahiyar, musamman a kasashe irin su Kenya, da Najeriya da kuma kasar Somalia. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China