A Najeriya a kalla mutane 7 sun rasa rayukansu, sakamakon wani hari da ake zagin wasu Fulani ne suka kaddamar da shi a kauyen Yangal, dake karamar hukumar Zango-Kataf ta jihar Kaduna.
Da yake yiwa manema labaru karin bayani game da aukuwar lamarin, mukaddashin shugaban karamar hukumar Zango-Kataf Jonathan Asake, ya ce, an shaida masa aukuwar harin ta wayar tarho a daren ranar Talata, lamarin ya sanya shi garzayawa kauyen na Yangal domin kai dauki.
Asake ya ce, sun mika gawawwakin mutane 5 zuwa asibiti, kana wasu mutanen 2 sun rasu bayan an kai su asibiti, yayin da wasu 12 ke samun kulawar jami'an lafiya.
Ya ce, maharan sun riga sun tsere daga kauyen lokacin da suka isa domin kai dauki.
Jihar Kaduna dake arewacin Najeriya dai na cikin jihohin dake fama da tashe-tashen hankula a kai a kai, musamman masu alaka da kabilanci ko addini, lamarin da a lokuta da dama kai jefa al'umma, musamman ma mata da yara kanana cikin mawuyacin hali. (Saminu)