in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An saki babban jami'in gwamnatin Libya da aka yi garkuwa da shi
2015-03-17 10:08:22 cri

Rahotanni daga Tripoli, babban birnin kasar Libya sun tabbatar da cewar, a ranar Litinin din aka sako ministan watsa labaran gwamnatin dake ikirarin ita ke rike da kasar, Ali Al-Huni bayan da wassu 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi na tsawon kwanaki 5 a cikin birnin.

Wata majiya a ma'aikatar watsa labaran kasar da ta tabbatar wa kamfanin dillancin labaran Xinhua ta ce, an sako shi a wannan ranar bayan da aka dauke shi daga gidan shi kwanaki biyar da suka gabata, sai dai majiyar ba ta yi karin bayani game da ko an biya kudin fansa, ko kuma wani sharadi makamancin hakan kafin a sako shi ba.

A shekarar 2013 ma an taba sace tsohon firaministan ministan kasar Ali Zeidan, kuma a shekarar 2014, an taba yin garkuwa da tsohon mataimakin firaministan Abu Shagor, amma daga baya an sako su lafiya lau.

Kasar ta Libya dake arewacin Afrika tana fuskanatar tashin hankali da barazanar sace mutane da kisan kai tun bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Mu'ammar Gaddafi a shekarar 2011. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China