in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu a rikicin Sirte na Libya ya karu zuwa 12
2015-03-19 10:33:08 cri

Rahotanni daga Tripoli na kasar Libya na nuna cewa, adadin wadanda suka mutu sakamakon arangama da aka yi tsakanin sojojin Libyan Dawn da na kungiyar IS a garin Sirte ya karu zuwa 12 a ranar Laraban nan kamar yadda wata majiyar soji ta tabbatar.

Yan kungiyar IS ta kai harin ba zata a kan sansanonin tsaron Libyan, musamman ma a garin Nofaliya dake gundumar Sirte. Mutane 12 suka mutu sakamakon hakan bayan da wassu 4 da suka ji rauni da farko su ma suka rasu a ranar Laraban nan.

Ita ma kungiyar ta IS, a cewar majiyar tsaron, ta samu gaggarumin koma baya a wajen mayakan tada kayan aiki. Kamar yadda majiyar tsaro ta yi wa Xinhua bayanin za'a fitar da kiyasin hasarar da IS din ta yi daga baya.

Sojojin Libyan Dawn wadanda galibi ke kunshe da kungiyoyin addini dake da makamai a halin yanzu suna yin kokarin karbe ikon birnin na Sirte mai nisan kilomita 450 daga gabashin Tripoli, babban birnin kasar. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China