Wani babban jami'in hukumar zaben kasar Cote d'Ivoire ya ba da tabbacin cewar, za'a gudanar da zaben shugaban kasa na kasar a watan Oktobar wannan shekarar kamar yadda aka tsara.
Babban jami'in hukumar zabe ta kasar Sourou Kone ya bayar da wannan tabbacin ne jim kadan bayan ganawarsa da sabon wakili a kan yancin 'dan adam a kasar ta Cote d'Ivoire na MDD Mohammed Ayat.
Kone ya ce, za'a dauki dukanin matakin da ya dace domin tabbatar da cewar, duk 'dan kasar da ya isa kada kuri'a ya samu damar jefa kuri'arsa a lokacin zaben.
Kone ya kara da cewar, wakilin na MDD ya nuna gamsuwarsa game da matakan da kasar ta dauka na gudanar da zabe.
Zaben na Oktoba ana ganin zai taimaka wajen samar da kwanciyar hankali a kasar bayan da kasar ta fada cikin mummunan rikici a karshen zaben shekarar 2010 zuwa 2011. (Suwaiba)