Jam'iyyun adawa na kasar Cote d'Ivoire sun kafa wani kawance domin daura damara sosai wajen fuskantar zabubukan shekarar 2015, musammun ma zaben shugaban kasa, in ji wadannan jam'iyyun adawa a ranar Litinin.
Kawancen na kunshe da jam'iyyar RPC, jam'iyyar PDR da kuma jam'iyyar PIA. Henriette Lagou, Soko Gbalehi da kuma Kouassi Bile, dukkan shugabannin kawancen jam'iyyun adawar sun bayyana niyyarsu ta shiga dukkan zabubukan da za'a gudanar a kasar Cote d'Ivoire, da zummar karbe ikonsu na 'yan tsakiya. (Maman Ada)