Mahukuntan kasar Kenya sun bayyana dage taron hadin gwiwa,don gane da tattauna batutuwan da suka shafi maida dubban 'yan gudun hijirar kasar Somaliya zuwa kasarsu ta haihuwa.
Wata sanarwa da ta fito daga ofishin ministan harkokin wajen Kenyan ta ce, an dage wannan babban taro na yini biyu, da a baya aka shirya gudanarwa a ranekun 28 zuwa 29 ga watan Agustan nan ne, domin baiwa hukumomin Somaliya damar shiryawa tsaf domin karbar 'yan gudun hijirar.
Har ila yau, taron na hadin gwiwa tsakanain gwamnatocin kasashen Kenya, da Somaliya, da ofishin babban kwamishinan MDD mai lura da harkokin 'yan gudun hijira da kuma kungiyoyin kasa da kasa da abin ya shafa, na da manufar share fagen inganta rayuwar 'yan gudun hijirar bayan komawarsu yankunansu na asali.
Kasar kenya dai ta karbi 'yan gudun hijirar da yawansu ya kai kimanin mutane 650,000 daga sassan gabashin Afrika, da na yankuna masu makwaftaka da manyan tafkunan yankin. Ita ce kuma ke da sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a Dadaab dake arewacin kasar.
An kuma kiyasta cewa, kimanin mutane 500,000 ne suka yi kaura daga Somaliya zuwa kasar ta Kenyan, adadin da ke kuma ci gaba da karuwa sakamakon fari da yawan barkewar rigingimu a Somaliyan. (Saminu)