Masu binciken cututtuka na kasar Sin sun gano banbance-banbancen dake akwai, game da nau'o'in kwayoyin cutar Ebola da suka yi gwaji a kan su, bayan barkewar cutar a kasar Saliyo.
Sakamakon binciken wanda aka wallafa a wata mujallar kimiyya, ya nuna cewa, kwayoyin cutar Ebola na da nau'o'i da dama, da kuma sauye-sauyen halittunsu, wanda hakan ke nuni ga asalinsu.
Masu binciken dake aiki a wata cibiyar nazarin kwayoyin cututtuka dake nan birnin Beijing, sun nazarci nau'o'in wannan cuta har 175, wadanda aka samo daga yankuna 5 na kasar ta Saliyo, tsakanin watannin Satumba zuwa Nuwambar bara, lokacin da cutar ke tsaka da yaduwa.
Binciken nasu ya kuma shaida yadda kwayoyin cutar suka fadada ta fannin nau'o'i, sai dai duk da hakan kwayoyin cutar na kama da irin wadanda aka samu a baya yayin barkewar cutar a lokutan da suka shude. (Saminu)