in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zuma zai jagoranci tawagar Afrika ta Kudu zuwa taron koli na AU
2014-06-23 13:41:48 cri

Shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma zai jagoranci tawagar kasarsa zuwa zaman taron da aka saba yi, na karo na 23 na taron kolin kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU.

Taron wanda za'a yi a Equatorial Guinea, a karkashin taken "shekarar 2014, shekara ta bunkasar noma da samar da wadatar abinci a Afrika, domin tunawa da zagayowar shekaru 10 na cikakken shirin bunksa noma a Afrika".

Ana sa rai, daga cikin abubuwan da taron kolin zai tattauna, akwai maganar matsayin zaman lafiya da tsaro a Afrika, da kuma kaddamar da sabbin ayyukan hadin kai, na ci gaban Afrika, da kuma matsayin Afrika a kan ajandar bayan shekara ta 2015, taron zai kuma duba rahoton kwamitin shugabannin kasashe da gwamnatoci na Afrika a kan lamarin canjin yanayi. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China