in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gabatar da shawarwari 5 a yayin taron karfafa hadin gwiwa tsakanin kasashen Asiya da Afirka
2015-04-13 20:25:46 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya halarci bikin bude taron shekara-shekara, na kungiyar tattaunawa game da harkokin doka na nahiyoyin Asiya da Afirka, wanda aka shirya gudanarwa a nan birnin Beijing, inda ya gabatar da jawabi.

Cikin jawabin nasa, ya ce a taron Bandung da ya gudana shekaru 60 da suka gabata, an tabbatar da ka'idoji 10 na daidaita dangantaka tsakanin kasa da kasa, kuma "gama kai, da zumunci da hadin gwiwa" kasancewar su tamkar hajoji masu matukar daraja ga kasashen duniya.

Ya ce a halin da ake ciki yanzu, ya kamata kasashen Asiya da Afirka su ci gaba da bin ruhin taron Bandung, domin tabbatar da shimfida zaman lafiya, da bunkasuwa, da adalci a dukkanin duniya. Kaza lika Mr. Li ya yi fatan cewa kasashen Asiya da na Afirka, za su kokarta wajen tabbatar da ganin tsarin siyasar kasa da kasa ya samun karin adalci, tare da kara bude kofa ga sauran kasashen duniya a lokacin da ake bunkasa tattalin arziki bisa tsarin da aka amince da shi.

Bugu da kari, ya yi fatan kasashen Asiya da Afirka, za su kara kokartawa wajen kare burin wanzuwar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankuna da shiyya-shiyya, har ma a duniya baki daya, ta yadda za su iya tinkarar kalubaloli sabbi cikin hadin gwiwa, da kara hada kai, da musaya a fannin dokokin kasa da kasa. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China