in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya jinjinawa aikin cibiyar fasahar sadarwa a Beijing
2015-05-08 10:07:01 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jinjinawa aikin kafa cibiyar fasahar sadarwa ta kasar Sin da ake gudanarwa a unguwar Zhongguancun, wadda ke arewa maso yammacin birnin Beijing, aikin da ya ce zai habaka fannin samar da sana'o'i da kere-kere.

Mr. Li wanda ya bayyana hakan yayin wata ziyara da ya kai yankin, ya kuma saurari tsokaci daga masu sha'awar harkokin fasahar zamani, da injiniyoyi a dakin shan kofi na 3W dake unguwar ta Zhongguancun, inda ya yi kira gare su da su kara kwazo, wajen aiwatar da kyakkyawar basirar da suke da ita ta hanyoyin da suka dace.

Ya ce, a wannan gaba da kasar Sin ke daga matsayin tsare-tsarenta na ci gaba, batutuwan da masanan suka ambata, za su zamo tamkar sa-kaimi ga ayyukan kirkire-kirkire, da kuma cin gajiyar tattalin arziki mai kunshe da tasirin ilimin zamani.

Firaminstan na Sin ya kara da cewa, duk da tafiyar wahainiya da ake fuskanta a fannin habakar tattalin arzikin kasar Sin, tagomashi daga harkar sana'o'i tsakanin matasa na da ma'anar gaske ga ci gaban kasar.

Wasu alkaluma da aka fitar sun nuna karuwar neman lasisin lambobin mallaka na sana'o'i a kasar ta Sin, da kaso 40 bisa dari cikin watannin 3 na farkon shekarar 2014 da ta gabata. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China