A jiya ne sojojin Najeriya da ke yaki da mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin kasar suka yi nasarar cafke wasu mutane uku da suka kware wajen hada bam a jihar Gombe, yayin wani samame da suka kaddamar a jihar.
Kakakin hedkwatar tsaron Najeriya Manjo janar Chris Olukolade wanda ya shaida hakan cikin wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya samu kwafe ya kuma bayyana cewa, mutanen da aka damke ana zaton 'ya'yan kungiyar Boko Haram ne da ke kokarin neman wuraren da za su kai hare-harensu, bayan da aka tarwatsa su daga sansanoninsu da ke dajin Sambisa.
Ya ce, kayayyakin da aka samu daga wajen su sun hada da babur mai kafa uku, da sauran kayayyakin hada abubuwan fashewa. Kuma yanzu haka ana yi musu tambayoyi.
Manjo Olukolade ya kara da cewa, dakarunsu sun himmatu wajen gudanar da bincike a dukkan fadin kasar don tabbatar da cewa, an dakushe duk wani kokarin mayakan kungiyar, ko sauran kungiyoyin 'yan ta'adda na kawo cikas ga shagulgulan mika mulki a fadin kasar. (Ibrahim)