Gwamnatin kasar Afirka ta Kudu ta kaddamar da wani shiri na tsawon wata guda tsakanin matasa a wani kokari na kawo karshe nuna kin jinin baki da ke damun kasar.
A jawabinsa yayin kaddamar da bikin da ya gudana a Soweto da ke kudu maso yammacin birnin Johannesburg, minista a fadar shugaban kasar Jebb Radebe ya bukaci matasa da su taimaka wajen kawo karshen wannan matsala ta nuna kin jinin baki.
Ya ce, a matsayinsa na 'yan Afirka kafin Turawan mulkin mallaka su raba kansu, akwai bukatar su hada kai don yin allah wadai da nuna wariyar launin fata, kuma batun nuna kin jinin baki ba shi da hurumi a tarihinsu da kuma nan gaba.
Don haka ya yi kira ga kowa da kowa, da ya taimaka wajen kawo karshen wannan aikin dabbaci na nuna kin jinin baki da nuna kyama a wannan kasa.
A watan Afrilun da ya gabata ne, rikicin kin jinin baki ya barke a kasar Afirka ta Kudu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar baki 'yan kasashen waje 7, kana wasu dubbai suka bar gidajensu, galibin su daga kasashen Afirka.
Sai dai mahukuntan kasar sun yi kokarin magance lamarin, bayan da suka baza jami'an tsaro a wuraren da rikicin ya fi kamari.(Ibrahim)