in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta Kudu ta shirya karbar WEF da zai gudana a nahiyar
2015-06-03 09:53:48 cri

Mahukuntan kasar Afirka ta Kudu sun bayyana cewa, sun kimtsa tsaf don karbar bakuncin taron dandalin tattalin arziki na duniya (WEF) karo na 25 da aka shirya gudanarwa a nahiyar.

Mai rikon mukamin kakakin majalisar zartarwar kasar Phumla Williams wadda ta shaida hakan ga manema labarai ta ce, ana sa ran taron na wannan karo zai samu halartar shugabannin 'yan kasuwa, siyasa da malaman jami'o'i da kungiyoyin fararen hula da kafofin watsa labarai daga ciki da wajen kasar sama da 1,000.

Taron da zai gudana daga ranar 3 zuwa 5 ga watan Yunin wannan shekara zai dora ne kan muhimman batutuwa guda uku da suka shafi kasuwanni masu tasowa, hako ma'adinai, da batun kirkire-kirkire, baya ga nuna irin damammakin da Allah ya horewa nahiyar Afirka, daya daga cikin shiyyoyin da ke bunkasa cikin sauri a duniya.

A ranar 4 ga watan Yuni ne ake sa ran shugaba Zuma na Afirka ta Kudu zai yi jawabi a taron, inda zai bayyana yadda kasar da ke daukar bakuncin taron na WEF na wannan shekara ta bude kofofinta na harkokin kasuwanci ga duniya.

A shekarar 1990 ne kasar Afirta ta Kudu ta fara karbar bakuncin wannan taro, shekarar da aka sako zababben shugaban kasar na farko na mulkin demokiradiya marigayi Nelson Mandela daga gidan yari. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China