Rundunar tsaron Nigeriya ta ce, sojojinta suna ta kara kashe 'yan ta'adda mayakan Boko Haram a samamen da suke ta kaiwa a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar. Kakakin rundunar Manjo Janar Chris Olukolade a cikin wata sanarwa da aka fitar wa manema labarai ya bayyana cewa, har ila yau an kwace makamai da dama daga sansanonin 'yan ta'addan da suka hada da babban bindiga guda daya, da kanana 13, gurneti na harbo roka da kuma sauran albarusai iri iri.
A cewar shi, an samu dubban takardun kudi na Euro a jikin wani kwamandansu da aka kashe sakamakon nasara samamen da aka kai a garin Mafa da ke kan iyaka da kasar.
Janar Olukolade ya ce, kwamandan da aka kashe wanda har ila yau shi ne a matsayin Amir, kuma 'dan kasan waje yana daga cikin 'yan ta'addan 30 da suka mutu lokacin samamen, sauran kuma suka tsere da raunuka masu tsanani.
An kuma samu mota kirar Toyota daga wajen 'yan ta'addan, sannan kuma motocin sulken su guda biyu an lalata su a lokacin gumurzun.
Yana mai bayanin cewa, abin da kawai suka yi asara daga nasu bangaren gwamnati shi ne wani kayan aikinsu da aka lalata, ya tabbatar da cewa, wannan samame ana nan ana ci gaba da shi a dukkan maboyan 'yan ta'addan da ake kan ganowa. (Fatimah)