in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta bankado shaidun yawaitar cin zarafin yara
2014-09-05 10:18:04 cri

A karon farko MDD ta fitar da wasu tarin shaidu a ranar Alhamis da ke nuna yadda ake cin zarafin yara a sassan daban-daban na duniya.

Sabon rahoton wanda asusun tallafawa yara na MDD (UNICEF) ya fitar ya gano cewa, kimanin kashi 2 bisa 3 na yaran da ke tsakanin shekaru 2 zuwa 14 da yawansu ya kai biliyan daya a duniya baki daya ne ke fuskantar cin zarafi daga wadanda suke yiwa hidima.

Rahoton ya ce, a shekara ta 2012 kadai, kimanin yara 95,000 ne suka mutu sakamakon lalatar da aka yi da su, amma duk da haka yaran sun fi fuskantar cin zarafi daga hannun wadanda suke yiwa hidima.

Har ila rahoton ya wallafa cewa, kimanin yara 'yan mata miliyan 120, 'yan kasa da shekaru 20, ne aka yiwa fyade ko wani nau'i na cin zarafi.

A cikin rahoton asusun na UNICEF, ya bayyana wasu dabaru da za su taimaka wa al'umma, gwamnatoci da kuma iyalai, wajen rage yadda ake cin zarafin yara, dabarun da suka hada da tallafa wa iyaye, samar da dabarun kare kai ga yara, canjin halayya, karfafa tsarin shari'a da dokokin yaki da manyan lafuffuka, tattara shaidu da ilimantar da jama'a game da cin zarafin yara, da kuma illolinsa ga harkokin rayuwa, da tattalin arziki, ta yadda za a canza halayyar jama'a. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China