in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana cin zarafin yara a lokutan yaki ba tare da hukunta masu laifi ba
2014-07-02 14:11:21 cri

An gano cewa, ana cigaba da cin zarafin yara kanana a duk lokacin da ake tashin hankali, ba tare da an hukunta masu aikata hakan ba, kamar yadda wata jami'ar MDD ta yi gargadi a ranar Talatan nan tare da kira ga hada hannu daga kasashen duniya baki daya da su ba da kariya ga yara daga wannan mummunan dabi'a da masu aikata hakan.

Leila Zerrougui wakiliya ta musamman a kan yara kanana game da fadace-fadace da suka hada da makamai ta sanar da hakan a lokacin da take gabatar da wani rahoto na shekara shekara na Ban Ki-moon a kan yara kanana da tashin hankalin da ya hada da makamai.

Rahoton da aka fitar a wannan rana na Talata ya nuna cewa, an shigar da yara kanana cikin ayyukan yaki tare da amfani da su, ana hallaka wassu, wadansu kuma an nakasa wasu, ban da wadanda ake keta hakkinsu da karfin tsiya tare da sauran ayyukan da ba su kamata ba a kusan kasashe 23 a shekarar bara kawai.

A cikin rahoton, an lissafa wadanda suka fi aikata wannan mummunan aiki da ya saba wa dokar kasa da kasa a kan yara kanana. Wannan sabon rahoton da aka fitar bana ya kara sunayen kungiyoyi guda 8 a cikin masu aikata wannan mugun dabi'a da suka hada da ta Boko Haram a Nigeriya wadanda suke kai hare-hare a kan makarantu suna kashe yara tare da nakasa wadansu.

Sai dai a wannan rahoton, an fitar da sunan sojojin kasar Chadi bayan da majalissar ta hada rahotonta ta kuma tabbatar da cewa, ba a dauki yara kanana a cikin sojojin kasar ba, sannan kuma an fitar da wadanda ke ciki lokacin da aka yi aikin bincike da saido a kan su.

Rahoton da Leila Zerrougui ta gabatar ya kuma tabbatar da cewa, ana bin wani sabon salon wajen saka kananan yara cikin sojojin kasar Afrika ta Tsakiya CAR, sannan take hakkin yara daga bangarori daban daban, ana ci gaba da aikata shi ba tare da an hukunta masu laifi ba. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China