in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Najeriya sun ceto mata da kananan yara 1000 a hannun Boko Haram
2015-05-08 10:24:41 cri

Rahotanni daga Najeriya na tabbatar da cewa, sojojin kasar sun yi nasarar ceto mata da kananan yara 1000 daga hannun mayakan Boko Haram.

Senata Ali Ndume, 'dan majalisar dattawa daga jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya da ke fama da rikicin Boko Haram wanda ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Abuja, babban birnin Najeriya, ya kuma bayyana tabbacin cewa, nan ba da dadewa ba ayyukan kungiyar za su zama tarihi.

Ya ce, muhimmin aiki na gaba bayan kakkabe mayakan Boko Haram shi ne kawar da nakiyoyin da suka binne a dajin Sambisa da gina hanyoyin shiga wasu kauyuka da kuma wasu muhimman wurare da abubuwan jin dadin rayuwa da 'yan tawayen suka lalata.

A watan Janairu ne kungiyar kula da kaurar jama'a ta kasa da kasa ta bayyana cewa, mutanen da suka bar gidajensu sakamakon rikicin na Boko Haram a Najeriya ya haura miliyan 1. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China