in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kira da a dauki kwararan matakai na hana hadurran bakin haure
2015-05-28 10:21:17 cri

Kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU ta yi kira ga mambobinta da su sa kasashensu zama abin jawo hankali da kuma tsaro domin hana jama'ar su bukatar yin wahalallen tafiya mai cike da hadari domin neman rayuwa mai inganci.

Kungiyar ta yi wannan kiran ne a ranar Laraban nan a cibiyarta dake Adis Ababe, lokacin wani bikin tunawa da wadanda suka salwanta a wannan yunkuri na tsallakawa zuwa kasashen Turai wanda ya samu halartar manyan jami'an diplomasiyya, abokan huldar kungiyar ta AU, kungiyoyin kasashen waje, kungiyoyi masu zaman kansu, shugabannin addini da kuma wadanda a da su ma suka shiga cikin wannnan yanayi.

Da yake magana a bikin, Mustapha Sidiki Kaloko, kwamishinan walwalar jama'a na kungiyar ta AU ya bayyana damuwarsa a wannan tsari da matasa ke rasa ransu da wahalallen hanyar da suke bi don su bar kasashensu, su samu rayuwa mai inganci.

Kwamishinan ya jaddada bukatar dake akwai cikin gaggawa ta samar da mafita kuma mai dorewa domin hana irin wannan bala'i. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China