Sabon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, zai kai ziyara a ranakun Laraba da Alhamis a kasashen Nijar da Chadi a yayin da kungiyar Boko Haram ta sake fito da sunanta a cikin wani sabon bidiyonta.
Kakakin shugaban Najeriya, Garba Shehu, ya bayyana a cikin wata sanarwa a ranar Talata cewa, shugaba Buhari zai je kasashen Chadi da Nijar domin tattauna barazanar kungiyar Boko Haram.
Wannan ziyara ta kwanaki biyu za ta mai da hankali kan matsalar tsaro, in ji mista Shehu, tare da nuna cewa, Najeriya na bukatar taimakon kasashe makwabtanta domin cimma nasara kan kamfen da take yi na yaki da kungiyar Boko Haram wanda ayyukanta suka janyo asarar rayukan mutane fiye da dubu goma sha biyar tun daga shekarar 2009. (Maman Ada)