Kwamitin masu saye da sayarwa na kasar Benin ya yi kiran al'ummar kasar da su fito kwansu kwalkwata a ranar Jumma'a a kan titunan birnin Cotonou, hedkwatar tattalin arzikin kasar domin yin allawadai da katse katsen wutar lantarki da ruwa dake kamari da kuma karancin man fetur da kasar ke fama da shi.
Wannan fitowar al'ummar kasar a kan titunan kasar na da manufar kawo matsin lamba ga hukumomin kasar, in ji shugaban kwamitin, mista Robin Accrombessi a ranar Alhamis. A wadannan lokuta na baya bayan nan, birane da dama na kasar Benin an takaita musu gwargwadon wutar da za su sha, a yayin da 'yan kasar ke fuskantar yawan daukewar wutar lantarki a ko wace rana. (Maman Ada)