Wani jirgin ruwan kasar Sin mai dauke da Sinawa 6 da 'yan kasar Ghana 20 ya isa Tema, babbar tashar jiragen ruwan Ghana lafiya, bayan da aka yi fashin sa a watan Janairu.
Wata majiyar kamfanin dillancin labarai ta Xinhua dake ofishin huldar jakadanci na kasar Sin dake Ghana ta ce, jirgin kamun kifin na kasar Sin, da ake kira Lu Rong Yuan 917, wasu gungun barayin teku wadanda ba'a san ko su wane ne ba suka yi fashinsa a ranar 28 ga watan jiya.
Majiyar ta ce, babu zato babu tsammani sai barayin da suka yi fashin jirgin ruwan suka fice daga jirgin a ranar 3 ga watan Fabarairu ba tare da wani sanannen dalili ba, hakan ya sa jirgin ruwan ya koma gabar ruwan Ghana a cikin kwanciyar hankali.
Majiyar ta ce, da isar jirgin Tema, sai jakadan kasar Sin a Ghana Sun Baohong ta yi wa Sinawa da 'yan kasar Ghana dake cikin jirgi barka, kana kuma ta mika godiyarta ga hukumomin kasar Ghana da sauran kasashe da suka taimaka domin ceto jirgin.
Jakadan ta kuma yi kira a kan kamfanonin kamun kifi na kasar Sin da su yi taka tsan-tsan a yayin da suke kamun kifi a cikin ruwan kasar Ghana. (Suwaiba)